In a bold statement, the U.S. Ambassador to Israel, Mike Huckabee, declared that America does not need Israel’s approval to enter a ceasefire agreement with the Houthi rebels in Yemen.
“We don’t need Israel’s permission to stop the Houthis from targeting our ships,” Huckabee said during a live interview on Israel’s Channel 12 News.
This statement came just days after President Donald Trump announced a ceasefire deal with the Houthis—without informing Israeli officials, a move that rattled political circles in Tel Aviv.
Direct Threats to U.S. Citizens
Just 48 hours before the announcement, a Houthi missile struck near Israel’s Ben Gurion Airport, injuring civilians and halting many international flights. Hours later, the Houthis launched a drone towards Israel, but it was intercepted.
According to Huckabee, U.S. military response will be based solely on direct threats to American citizens, There are 700,000 American citizens living in Israel. If the Houthis injure even one of them, it becomes our business.”
Trump’s Calculated Silence
When asked if the U.S. would only act after American casualties, Huckabee replied, It depends on what makes it our issue in real time.
Trump, on his part, said he would “consider it if something happens,” indicating that American involvement hinges on developments, not Israeli pressure.
Since November 2023, the Houthis have launched repeated attacks on Israel and Red Sea ships, claiming support for Palestinians amid the Gaza war. In response, Israel has bombed Houthi infrastructure in Yemen, including airstrips and fuel depots in Sana’a and Hodeidah.
Meanwhile, the U.S. has carried out over 1,700 airstrikes across Yemen under Operation Rough Rider since March 15. One deadly strike on April 28 reportedly killed 68 people at a refugee center—one of the deadliest attacks so far.
THOUGHT-PROVOKING QUESTION:
Does this U.S.–Houthi ceasefire without Israel’s involvement cool down tensions—or light a new fire?.
By Gaskiyar Lammari – 09/05/2025
HAUSA:
Amurka Ta Ce: “Ba Sai Mun Tambayi Isra’ila ba Don Yin Sulhu da Houthi”
Amurka ta bayyanawa duniya cewa ba lallai bane ta nemi amincewar Isra’ila kafin ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da 'yan Houthi na Yemen. Wannan furuci na zuwa daga bakin jakadan Amurka a Isra’ila, Mike Huckabee, wanda ya ce:
“Ba sai mun nemi izni daga Isra’ila ba kafin mu hana Houthi harbin jiragen ruwanmu.”
Wannan magana ta fito ne jim kaɗan bayan da Shugaba Donald Trump ya sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta da ƙungiyar Houthi, ba tare da shawarwarin Isra’ila ba – lamarin da ya tayar da kura a bangaren Isra’ila.
Barazana Kai Tsaye ga Amurka
A cikin kwanakinnan, wani roka daga Houthi ya faɗi kusa da filin jirgin saman Ben Gurion a Isra’ila, ya raunata mutane tare da hana tashi da saukar jiragen ƙasashen waje. Cikin sa’o’i 24, Houthi suka sake harba jirgi mara matuki zuwa Isra’ila – duk da cewa an cafke shi kafin ya yi barna.
Amurka dai ta ce martaninta zai ta’allaka ne da barazanar da ke fuskantar ’yan ƙasarta. Hukabee ya fayyace haka:
“Muna da ’yan Amurka fiye da dubu 700 a Isra’ila. Idan aka kai musu hari, to lamarin ya shafe mu kai tsaye.”
Yarjejeniyar da Ta Girgiza Isra’ila
Yayin da Trump ke kokarin daidaita harkokin yankin, ya bayyana cewa zai maida hankali ne kawai idan wani abu ya faru da Amurka.
“Zan shiga tsakani idan wani abu ya faru,” in ji shi.
Tun Nuwamba 2023, Houthi na kai hare-hare kan jiragen ruwa da Isra’ila, suna mai da martani ne kan yakin da ake ci gaba da yi a Gaza. Isra’ila kuwa na mayar da martani da hare-haren sama a Yemen, musamman kan cibiyoyin su a Hodeidah da Sana’a.
A halin yanzu, Amurka ta kai fiye da hare-hare 1,700 tun daga Maris 15 a karkashin “Operation Rough Rider.” A harin da suka kai ranar 28 ga Afrilu, mutane 68 sun mutu, wanda hakan ya zama ɗaya daga cikin mafi muni a yakin.
TAMBAYA MAI TUNZURA TUNANI:
Shin wannan yarjejeniya tsakanin Amurka da Houthi, ba tare da Isra’ila ba, zai iya zama matakin rage rikici ne ko kuwa ƙara tayar da kura?
Daga Gaskiyar Lammari – 09/05/2025
0 Comments