Shugaban Rundunar Tsaron Iran, Janar Ahmad Rezaei Radan, ya jagoranci wata tawaga ta manyan jami'an tsaro zuwa Jamhuriyar Nijar, inda suka gana da Ministan Cikin Gida na ƙasar, a wani mataki na ƙarfafa dangantakar tsaro tsakanin ƙasashen biyu.
A ganawar da aka gudanar, bangarorin biyu sun amince da kafa wani kwamitin kwararru da zai rika gudanar da tattaunawa akai-akai kan batutuwan da suka shafi tsaro da zaman lafiya a yankin.
Haka kuma, an sanya hannu kan wata yarjejeniya ta hadin gwiwa da ta kunshi muhimman fannoni kamar haka:
– Yaki da ta’addanci
– Hana laifukan ƙetare iyaka
– Yaki da safarar miyagun kwayoyi
Jami’an biyu sun bayyana aniyar ƙasashensu na aiki tare don tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali, musamman a yankin Sahel da ke fama da matsalolin tsaro daban-daban
Creadt: Hoto: Nijar Hausa.
0 Comments