Ministan harkokin cikin gida na Nijar ya gana da shugaban jami’an tsaron Iran a Yamai, inda suka tattauna kan batutuwan tsaro da suka shafi ƙasashensu.
A yayin ganawar, an jaddada bukatar haɗin gwiwa tsakanin bangarorin tsaro, ciki har da musayar bayanai, horar da jami’ai, da kuma tsare-tsaren yaƙi da ta’addanci da fataucin miyagun ƙwayoyi.
An yanke shawarar kafa kwamiti na haɗin gwiwa da zai rika ganawa duk shekara don samar da ingantaccen tsarin aiki tsakanin ƙasashen biyu. Har ila yau, an amince da tura wasu jami’an tsaro daga Nijar zuwa Iran don horaswa.
Ƙungiyoyin biyu sun kuma yi nazari kan yadda za a inganta tsaro a yankunan iyaka da kuma batun ayyukan hadin gwiwa a matakin kasa da kasa.
A ƙarshe, an rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyi masu muhimmanci da kuma musayar kyaututtuka tsakanin wakilan ɓangarorin biyu.
0 Comments