Trump Meets Syrian President in Riyadh, Announces Sanctions Relief
Riyadh, Wednesday – U.S. President Donald Trump met with Syrian President Ahmad Al Shara in Riyadh, Saudi Arabia, on Wednesday. The meeting came just one day after President Trump announced his administration’s intention to lift economic sanctions previously imposed on Syria.
“I will issue a directive to suspend the sanctions imposed on Syria in order to give them a chance to rise and rejoin international affairs,” Trump said during an investment forum between the U.S. and Saudi Arabia held in Riyadh.
An official from the Turkish presidential palace confirmed to The National newspaper that Turkish President Recep Tayyip Erdogan also joined the meeting via video conference. Saudi Crown Prince Mohammed bin Salman and Syrian President Ahmad Al Shara were also in attendance.
The meeting marks a significant shift for Syria, which has been seeking to rebuild after years of conflict. It may also signal the beginning of the end of the era of former Syrian President Bashar Al-Assad, who had long faced international isolation and Western sanctions.
HAUSA
Trump ya gana da Shugaban Syria a Riyadh, ya sanar da dage takunkumi
Riyadh, Laraba – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya gana da Shugaban Syria, Ahmad Al Shara, a birnin Riyadh na kasar Saudiyya a ranar Laraba. Wannan ganawar na zuwa ne kwana guda bayan da Mista Trump ya sanar da aniyar gwamnatin sa na dage takunkumin tattalin arziki da Amurka ta kakabawa Syria.
"Zan ba da umarnin dakatar da takunkumin da aka kakaba wa Syria domin ba su damar samun daukaka da komawa cikin harkokin kasa da kasa," in ji Trump yayin wani taron zuba jari tsakanin Amurka da Saudiyya da aka gudanar a Riyadh.
Wani jami'in fadar shugaban kasar Turkiyya ya shaida wa jaridar The National cewa Shugaba Recep Tayyip Erdogan ma ya halarci ganawar ta hanyar yanar gizo. Haka zalika, Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, da shugaban Syria Ahmad Al Shara, sun halarci ganawar.
Ganawar na zaman wata babbar alama ta sauyin matsayi ga kasar Syria, wadda ke kokarin farfadowa daga rikicin da ya daɗe yana addabar ta. Wannan na iya nufin mataki na kawo karshen mulkin tsohon shugaban kasar, Bashar Al-Assad, wanda aka dade ana suka da takunkumi a kansa daga kasashen yamma.
 
0 Comments