BREAKING NEWS: Sule Lamido Says Nigerians Brought Hardship Upon Themselves
Abuja, Nigeria — Former Governor of Jigawa State, Alhaji Sule Lamido, has stated that the current economic hardship facing Nigerians is a result of their own choices. Speaking in an interview with BBC Hausa, he said he no longer feels pity for the people because they are responsible for their situation.
Lamido said: “Anyone who has a voter’s card, knows APC, knows PDP, knows their candidates, and still goes ahead to vote—who should he blame if not himself?” According to him, the poor decisions made by voters have directly led to today’s inflation and economic struggles.
He further stated that instead of constant complaints, citizens should turn to prayers and seek divine help to correct the mistakes they made at the polls. “If you know you’ve made a wrong choice during elections, then commit to prayer—perhaps you’ll be able to fix it next time,” he said.
When asked whether President Bola Ahmed Tinubu had ever reached out to him for advice on addressing the country’s challenges, Sule Lamido responded: “I have never been contacted, and I know I will not be contacted. Because that’s not the path this government is taking.”
HAUSA
DA DUMI-DUMINSA: Sule Lamido ya ce ‘Yan Najeriya ne suka jefa kansu cikin talauci da tsadar rayuwa
Abuja, Najeriya — Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya bayyana cewa halin kuncin da ƴan Najeriya ke ciki a yau, sakamakon zabin da suka yi da kansu ne. Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa, inda ya ce ya daina jin tausayin ƴan kasa saboda yadda suka jefa kansu cikin wahala.
Lamido ya ce: “Mutumin da yake da katin zabe, ya san jam’iyyar APC, ya san PDP, ya san yan takararsu, kuma da hannunsa ya kada kuri’a – to waye zai yi wa kuka idan ba shi kansa ba?” A cewarsa, rashin dacewar zabin da mutane suka yi ne ya haifar da matsin tattalin arziki da wahalhalun yau da kullum.
Ya kara da cewa maimakon mutane su rika koke-koke, kamata ya yi su ci gaba da yin addu’a domin samun ikon gyara kuskuren da suka yi a zabe. “Idan ka san ka yi kuskure wajen zabe, sai ka dage da addu’a, ko da kuwa a gaba za ka gyara,” in ji shi.
A lokacin da ɗan jarida ya tambaye shi ko Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taɓa tuntubar sa domin neman shawara wajen shawo kan matsalolin da Najeriya ke fama da su, Sule Lamido ya ce: “Ba a taɓa nemana ba, kuma nasan ba za a nemeni ba. Domin ba a kan wannan tafarkin aka dauka ba.”
0 Comments