New Diplomatic Efforts: UAE Mediates Secret Talks Between Syria and Israel
Reports indicate that secret negotiations are underway between Syria and Israel, with the United Arab Emirates (UAE) playing a key mediating role. These talks are centered around issues of security and intelligence, aiming to ease tensions and build mutual understanding between the two nations, which currently have no formal diplomatic ties.
The discussions reportedly began shortly after Syrian President Ahmed Sharaa visited Abu Dhabi on April 13. According to sources, the focus has been on counterterrorism efforts, though sensitive military issues—especially concerning Israeli military operations inside Syria—were also addressed.
This development comes in the wake of recent Israeli airstrikes on Syrian territory, including one that targeted an area near the presidential palace in Damascus. President Sharaa has expressed his commitment to national unity and signaled a desire to assure Israel that Syria poses no threat. Among the steps taken is the detention of members of the Palestinian Islamic Jihad group allegedly involved in recent attacks.
HAUSA
Sabon Yunƙuri Tsakanin Siriya da Isra’ila: Hadaddiyar Daular Larabawa Na Tsaka-tsaki a Tattaunawar Sirri
Wasu rahotanni sun bayyana cewa ana gudanar da muhimman tattaunawa a sirrance tsakanin Siriya da Isra’ila, karkashin jagorancin Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE). Tattaunawar na mai da hankali ne kan batutuwan tsaro da harkar leken asiri, da nufin rage rashin jituwa da gina wata sabuwar fahimta tsakanin bangarorin biyu da ba su da huldar diflomasiyya kai tsaye a halin yanzu.
An fara wannan shirin ne bayan ziyarar da shugaban kasar Siriya, Ahmed Sharaa, ya kai birnin Abu Dhabi a ranar 13 ga Afrilu. A cewar majiyoyi, bangarorin sun fi karkata kan yaki da ta’addanci, kodayake an tabo batutuwa masu nauyi na tsaro, musamman ayyukan sojin Isra’ila da ke faruwa a cikin Siriya.
Wannan mataki ya zo a daidai lokacin da Isra’ila ta kai wasu hare-hare kwanan nan a yankunan Siriya, ciki har da wanda ya faru kusa da fadar shugaban kasa da ke Damascus. Sabon shugaban kasar Siriya ya bayyana cewa yana son ganin an daidaita kasar, tare da tabbatar wa Isra’ila cewa ba su da wata barazana daga bangarensa. Daga cikin matakan da ya dauka har da kama wasu daga cikin mambobin kungiyar Jihad Islama ta Falasdinawa da ake zargi da hannu a hare-haren baya-bayan nan.
0 Comments