Recent reports reveal that the United States and Israel are in discussions about establishing a transitional administration led by the U.S. to govern Gaza after the ongoing war. The aim of this administration would be to restore peace and demilitarize the territory before handing over control to a capable Palestinian government.
Some Israeli officials are exploring strategies that include dividing Gaza into security zones and setting up permanent military bases—raising further concerns about the region’s future.
The plan resembles the U.S.-led authority established in Iraq after the 2003 invasion, which faced heavy criticism before power was handed over in 2004. This time, other countries may join the transitional process, though no names have been mentioned. Notably, neither Hamas nor the Palestinian Authority (PA), which currently governs parts of the West Bank, would be included.
Critics warn that such a move could trigger unrest and political backlash, especially if it is seen as a foreign occupation.
In response, a U.S. State Department spokesperson stated: “We want peace and the immediate release of the hostages. Our principles remain firm—support for Israel and the pursuit of peace.”
Israeli Prime Minister Netanyahu and his officials have not commented on the issue.
Israeli Foreign Minister Gideon Saar has suggested that a transitional period may involve moderate Arab nations, but emphasized that Israel does not wish to control the civilian lives of Gazans—its focus is strictly on security.
Hamas has outright rejected any foreign-led administration. “The people of Gaza should choose their own leaders,” said Ismail Al-Thawabta, head of Hamas’ media office in Gaza.
Meanwhile, the United Arab Emirates (UAE) has proposed an international coalition to govern Gaza, on the condition that it includes the PA and offers a clear path to Palestinian statehood. However, the Israeli government opposes PA involvement and rejects Palestinian sovereignty.
As the war rages on and Israel continues its offensive in an attempt to rescue remaining hostages, Gaza’s health ministry reports that over 52,000 people have lost their lives.
At the same time, some Israeli lawmakers are proposing highly controversial measures—such as the mass relocation of Gaza’s population and the rebuilding of Jewish settlements in the enclave. These proposals are intensifying concerns about the region’s long-term stability.
HAUSA:
LABARI DA ƊUMI-ƊUMIN SA: Tattaunawa Tsakanin Amurka da Isra’ila Kan Gudanar da Gaza Bayan Yakin
Wasu rahotanni sun nuna cewa Amurka da Isra’ila na tattaunawa kan yiwuwar kafa wata rikon kwarya da Amurka za ta jagoranta domin gudanar da Gaza bayan yakin da ke gudana. Wannan tsarin na nufin samar da zaman lafiya da kwantar da tarzoma kafin a mika mulki ga wata gwamnatin Palasɗiniyya da za ta iya jagoranci.
Wasu jami’an Isra’ila suna nazarin dabarun da suka hada da raba Gaza zuwa yankunan tsaro da kuma gina sansanonin soja na dindindin, lamarin da ke kara haifar da damuwa kan makomar yankin.
An ce wannan shiri yana da kama da tsarin da Amurka ta kafa a Iraki bayan harin 2003, wanda ya fuskanci suka sosai kafin a mika mulki a 2004. Wannan karon, wasu kasashe za su iya shiga cikin rikon kwarya, amma ba a fadi sunayen kasashen ba. Sai dai an ce babu shirin hada da Hamas ko kuma gwamnatin PA da ke kula da yankin Yammacin Kogin Jordan.
Masu suka suna gargadi cewa idan aka dauki wannan mataki, zai iya haddasa fargaba da tashe-tashen hankula, musamman idan aka dauki tsarin a matsayin mamayar waje.
A martaninsa, kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ya ce: “Muna so a samu zaman lafiya da sakin fursunoni nan take. Manufofinmu sun tsaya akan goyon bayan Isra’ila da kuma neman zaman lafiya.”
Firayim Minista Netanyahu bai ce komai ba kan batun, haka ma wasu daga cikin jami’ansa.
Ministan Harkokin Wajen Isra’ila, Gideon Saar, ya taba cewa ana iya kafa wani tsarin rikon kwarya tare da kasashen Larabawa masu matsakaicin ra’ayi. Amma ya jaddada cewa Isra’ila ba ta sha’awar gudanar da rayuwar fararen hula a Gaza—tsaro ne kawai a gabanta.
Hamas ta bayyana kin amincewarta da duk wani shiri na gudanar da Gaza daga waje. “Mutanen Gaza ne za su zabi shugabanninsu,” in ji kakakin ofishin yada labaran Hamas, Ismail Al-Thawabta.
Amma duk da haka, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) ta gabatar da wata shawara ta kafa hadin gwiwar kasa da kasa domin gudanar da Gaza, bisa sharadin cewa a hada da PA da kuma samar da sahihin hanya zuwa kafa kasar Palasɗinu. Sai dai Isra’ila ta nuna kin amincewarta da hakan.
Yayin da yakin ke ci gaba, Isra’ila na kara matsa lamba domin ceto fursunonin da ke hannun Hamas. Rahotanni daga ma’aikatar lafiya ta Gaza sun nuna cewa sama da mutane 52,000 sun riga mu gidan gaskiya.
A gefe guda, wasu daga cikin ‘yan majalisar Isra’ila na mika ra’ayoyi masu rikitarwa, irin su korar daukacin al’ummar Gaza da sake gina wuraren Yahudawa a cikin Gaza. Wadannan tsare-tsare suna kara tada jijiyoyin wuya kan makomar yankin.
0 Comments