Macron: The Situation in Gaza Is a “Terrible Disaster” and “A Disgrace”

Picture ® Creadt Google Search 🔍

Macron: The Situation in Gaza Is a “Terrible Disaster” and “A Disgrace”

In an interview on Tuesday, French President Emmanuel Macron expressed deep concern over the humanitarian situation in Gaza, describing it as a "terrible disaster" and "unacceptable."

“There is no water, no medicine. We can't evacuate the wounded. Doctors can't get in,” Macron said in an interview with TF1.

He called the situation “a disgrace,” urging for the immediate reopening of humanitarian aid corridors.

The president stressed that the most viable path to resolving the conflict is through a political solution that allows Palestinians and Israelis to live side by side in mutual understanding.

When asked whether the term “genocide” was appropriate to describe the events, Macron responded that it should be left to historians to decide.

“It is not the role of a head of state to say ‘this is genocide’ or ‘this is not’,” he said.

Regarding European cooperation agreements with Israel, Macron indicated he is “open” to reassessing them, including the possibility of sanctions, adding:

“We cannot pretend nothing is happening. We must increase pressure.”

HAUSA:
Macron: Halin da ake ciki a Gaza “mummunan bala’i ne” kuma “abin kunya”

A wata hira da aka yi da shi a ranar Talata, Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana damuwarsa kan halin da ake ciki a Zirin Gaza, yana mai bayyana shi a matsayin "mummunan bala’i" da kuma "mara yarda."

“Babu ruwa, babu magunguna. Ba za a iya kwashe waɗanda suka jikkata ba. Likitoci ba za su iya shiga ba,” in ji Macron cikin wata hira da kafar TF1.

Ya bayyana cewa abin da ke faruwa “abin kunya ne”, yana mai kira da a gaggauta buɗe hanyoyin ba da agajin jin kai.

Shugaban ya jaddada cewa hanyar da ta fi dacewa don magance rikicin shi ne a cimma yarjejeniyar siyasa da za ta bai wa Palasdinawa da Isra'ilawa damar zaune tare cikin fahimta.

Da aka tambaye shi game da yiwuwar amfani da kalmar “kisan kare dangi” wajen bayyana lamarin, Macron ya ce wannan tambaya ya kamata a bar wa masana tarihi su tantance.

“Bai kamata shugaban kasa ya fadi cewa ‘wannan kisan kiyashi ne’ ko akasin haka,” in ji shi.

A kan batun alakar Turai da Isra’ila, Macron ya nuna cewa “a shirye yake” don sake nazarin yarjejeniyoyin hadin gwiwa, ciki har da yiwuwar kakabawa Isra’ila takunkumi, yana mai cewa:

“Ba za mu iya rufe ido muna cewa babu abin da ke faruwa ba. Dole ne mu kara matsa lamba.”


Post a Comment

0 Comments