BREAKING: BH Fighters Attack Soldiers in Adamawa, Kill Seven Civilians
BH fighters launched a deadly attack in Madagali town, Adamawa State, killing seven civilians. They also ambushed a group of soldiers, injuring four of them.
According to sources, the ambush happened around 4:00 PM on Thursday, while the soldiers were trying to evacuate the body of one of the civilians killed in the earlier attack. During the incident, the attackers seized four motorcycles belonging to the army.
Residents described the Wednesday night attack as terrifying. The insurgents reportedly stormed the town in large numbers, heavily armed, and began shooting randomly before being repelled by soldiers and local vigilantes.
This attack came just two days after top national security officials — including the National Security Adviser and heads of intelligence agencies — visited Adamawa to meet with Governor Ahmadu Umaru Fintiri over the security situation.
There are also reports that the attackers raided Hong Local Government Area, killed civilians, and destroyed food supplies, raising fears of a larger coordinated assault.
Tension is rising in farming communities near the Borno border, where residents are fleeing their homes in fear of more attacks.
As of the time of this report, the Nigerian Army has not confirmed the incident, and calls and messages sent to their spokesperson remain unanswered.
HAUSA
Mayakan BH sun kai hari kan sojoji a Adamawa, sun kashe mutane bakwai
Mayakan BH sun kai hari a garin Madagali, Jihar Adamawa, inda suka kashe fararen hula bakwai. Haka kuma sun yi kwanton-bauna ga wasu sojoji, lamarin da ya jikkata sojoji hudu.
An kai harin kwanton-bauna da misalin ƙarfe 4 na yamma ranar Alhamis, lokacin da sojoji ke ƙoƙarin ɗaukar gawar ɗaya daga cikin fararen hular da aka kashe a harin farko. A cewar majiyoyi, mayakan sun kwace babura huɗu mallakin rundunar soji yayin harin.
Mazauna garin sun bayyana cewa harin da aka kai da dare a ranar Laraba ya haifar da firgici, inda ‘yan ta’addan suka shiga da dama dauke da makamai masu ƙarfi, suka fara harbin kan mai uwa da wabi kafin dakarun soji da ‘yan sa-kai su fatattake su.
Harin ya biyo bayan ziyarar da manyan jami’an tsaro suka kai Adamawa, ciki har da mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro da shugabannin hukumomin leƙen asiri, inda suka gana da Gwamna Fintiri.
Har ila yau, an ruwaito cewa mayakan BH sun kai wani hari a ƙaramar hukumar Hong, inda suka kashe fararen hula tare da lalata abinci, abinda ya haddasa tsoron wani babban hari mai zuwa.
Tashin hankali na ƙaruwa a yankunan da ke iyaka da Jihar Borno, inda mutane ke tserewa daga gidajensu saboda tsoron hare-hare.
Rundunar sojin Najeriya ba ta ce komai ba kan lamarin a halin yanzu, kuma ba a samu amsa daga mai magana da yawunsu ba har zuwa yanzu.
0 Comments