Trump Says Iran Is Ready for Nuclear Deal, Urges Swift Action

Trump Says Iran Is Ready for Nuclear Deal, Urges Swift Action

U.S. President Donald Trump stated on Friday that Iran appears willing to reach a nuclear agreement, while urging Tehran to act quickly before consequences arise.

“They’ve made a decision. Most importantly, they know they need to move fast—or something bad will happen,” Trump told reporters aboard Air Force One after departing the United Arab Emirates, according to AFP.

A day earlier, Trump mentioned that Washington was close to finalizing a deal with Tehran, following comments from an Iranian official suggesting Iran was open to an agreement involving a trade-off for sanctions relief.

Since April 12, the U.S. and Iran have engaged in four rounds of indirect talks mediated by Oman. Both sides have described the discussions as constructive and promising.

HAUSA:
Trump ya ce Iran ta nuna aniyar yarjejeniyar nukiliya, ya bukace ta da ta gaggauta cimma matsaya

Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana a ranar Juma’a cewa Iran na da niyyar kulla yarjejeniya kan batun nukiliya, tare da yin gargaɗi ga gwamnatin Tehran da ta hanzarta kammala tattaunawar.

A cewarsa, "Sun riga sun yanke shawara. Abu mafi muhimmanci shi ne, sun san cewa lokaci yana guje musu—kuma idan ba su yi sauri ba, to wani abu mara daɗi na iya faruwa." Trump ya bayyana hakan ne ga manema labarai a cikin jirgin Air Force One bayan tafiyarsa daga Hadaddiyar Daular Larabawa.

A ranar Alhamis da ta gabata, Trump ya ce gwamnatin Amurka na dab da cimma wata yarjejeniya da Iran, biyo bayan jawabin wani jami’in gwamnatin Iran da ya nuna shirinsu na musayar sassauta takunkumi da wata yarjejeniya.

Tun ranar 12 ga watan Afrilu ake ci gaba da zagaye na hudu na tattaunawa tsakanin Amurka da Iran, karkashin jagorancin Oman. Dukkan ɓangarorin biyu sun bayyana cewa ana samun ci gaba mai ma’ana.

Post a Comment

0 Comments