TINUBU & SHETTIMA LEAD $25 BILLION GAS PIPELINE PROJECT TO EUROPE

TINUBU & SHETTIMA LEAD $25 BILLION GAS PIPELINE PROJECT TO EUROPE

Abuja, Nigeria – In a landmark move to reposition Nigeria’s energy influence on the global stage, President Bola Ahmed Tinubu and Vice President Kashim Shettima have emerged as key drivers behind a massive $25 billion offshore gas pipeline project linking Nigeria to European markets.

Vice President Shettima disclosed this on Monday during a high-level meeting with executives from Vitol Group — a global leader in energy trading — held at the Presidential Villa in Abuja.

Shettima described the initiative as a strategic leap towards economic transformation, emphasizing the growing confidence of international investors in Nigeria’s evolving energy sector.

“Leadership is central,” Shettima remarked. “President Tinubu rose from the fields of energy and finance. His deep understanding of these sectors makes this an extraordinary time for global investors.”

The pipeline, once completed, is expected to reposition Nigeria among the top energy suppliers globally, strengthen international partnerships, and significantly increase foreign revenue from gas exports.

The project underscores the Tinubu-Shettima administration’s commitment to meaningful investment and visionary leadership as a catalyst for economic reform.

HAUSA
TINUBU & SHETTIMA SUN ZAMO JIGO A SHIRIN BUTUTUN GAS NA DALA BILIYAN 25 ZUWA TURAI

Abuja, Najeriya – A wani mataki na tarihi wajen sauya fasalin tattalin arzikin Najeriya da ƙarfafa tasirinta a fannin makamashi, Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima, sun zamo jigo a wani katafaren aiki na gina bututun gas mai darajar dala biliyan 25 da zai tashi daga Najeriya ya isa kasashen Turai.

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima ne ya sanar da haka ranar Litinin yayin wata ganawa da manyan jami’an kamfanin Vitol Group — kamfani na duniya da ke jagorani a kasuwancin makamashi — a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Shettima ya bayyana aikin a matsayin wani ginshiki na sauya fasalin tattalin arziki tare da tabbatar da yadda gwamnatin Tinubu ke jawo hankalin masu zuba jari daga kasashen waje. 

Ya jaddada cewa sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ta fara sun haifar da yanayi mai kyau da ya karfafa gwiwar kamfanoni da masu jarin kasa da kasa.

"Jagoranci shi ne jigo," in ji Shettima. “Shugaba Tinubu ya fito ne daga masana’antun makamashi da kuɗi, kuma fahimtarsa mai zurfi a wadannan fannonin na daga cikin manyan dalilan da yasa wannan lokaci ya zama na musamman ga masu saka jari.”

A cewar rahotanni, aikin na bututun gas zai ƙarfafa matsayin Najeriya a kasuwar makamashi ta duniya, ƙara karɓuwa a kasashen waje da kuma kara samun kuɗin shiga daga fitar da iskar gas zuwa Turai.

Wannan mataki na kara tabbatar da cewa gwamnatin Tinubu-Shettima na da niyyar cika alkawuran sauya tattalin arziki ta hanyar manyan ayyuka masu tasiri da kuma shugabanci mai hangen nesa.

Post a Comment

0 Comments