185 Students Graduate with Complete Qur’an Memorization at Fudiyya School in Fagge

185 Students Graduate with Complete Qur’an Memorization at Fudiyya School in Fagge

Fagge, Kano – Joy and pride filled the hearts of parents and teachers as students of Fudiyya School in Fagge Local Government Area celebrated their successful completion of the Holy Qur’an.
In this 14th graduation ceremony, 185 students were honored for memorizing the entire Qur’an, a remarkable spiritual and academic milestone that reflects discipline, dedication, and strong mentorship.

The school’s principal, Malam Ali Murtadha, expressed his delight over the achievement, stating:

"This is a historic day for our school. We are proud of our students and pray that they use their knowledge to benefit themselves and society."

Some of the graduating students attributed their success to perseverance, prayer, and the continuous support of their teachers and parents.
In his closing remarks, Malam Ali encouraged parents to continue supporting their children in both religious and modern education to help build a better future.

Report by: Khadija Abdul Wahab

HAUSA:
Daliban Makarantar Fudiyya a Fagge Sun Kammala Saukar Al-Qur’ani na 14
Fagge, Kano – Murna da alfahari sun cika zuciyar iyaye da malamai yayin da daliban makarantar Fudiyya da ke Fagge suka kammala saukar Al-Qur’ani a karo na 14.

A cewar shugabannin makarantar, dalibai 185 ne suka haddace Al-Qur’ani daga farko har ƙarshe. Wannan babban nasara ce da ke nuna jajircewar ɗaliban da kuma himmar malamai wajen cusa ilimi da tarbiyya.

Shugaban makarantar, Malam Ali Murtadha, ya bayyana cewa wannan rana tarihi ce ga makarantar. Ya ce:

"Muna alfahari da wannan nasara. Allah ya ba su ikon amfani da ilimin da suka samu wajen inganta kansu da al’umma."

Wasu daga cikin daliban da aka tattauna da su sun bayyana cewa sadaukarwa, dagewa, da addu’ar iyaye da malamai ne suka taimaka musu.

A ƙarshe, Malam Ali ya yi kira ga iyaye da su ci gaba da ƙarfafa wa ‘ya’yansu guiwa wajen neman ilimin addini da na zamani domin samun ingantaccen makoma.
Rahoto daga: Khadija Abdul Wahab 

Post a Comment

0 Comments