I advise Nigerians not to rely solely on social media as a source of income. That’s a mistake. It’s better to have a strong skill or business and use social media to support it.
If you abandon everything else just because you think YouTube, Facebook, or a website will pay you, then you're wrong. One day, they can take everything down without warning, and you’ll be helpless.
For those trying to build a channel or website to earn money, don’t commit 100% without a plan. Even after building the platform, you may not get approval to earn from it.
Especially with YouTube and websites, getting monetization approval is difficult. You might spend 10 years building, and still not be approved. Sometimes, problems come up during the building phase, and later they tell you that you haven’t met the requirements.
For example, you might see ads on your YouTube channel, but you haven’t applied for AdSense. Others may assume you're getting paid, while you’ve never even applied. That causes confusion.
My advice: don’t let online work stop you from doing real business. If you do, you're deceiving yourself. Even if platforms start paying you, there's no guarantee. They can delete your account anytime.
Use social media mainly to share your message or promote your products. If later they start paying – Alhamdulillah. But if they don’t, you never relied on them to begin with.
HAUSA:
YouTube Facebook:
Ina ba da shawara ga 'yan Najeriya cewa kada su dogara da Social Media kawai a matsayin hanyar samun kuɗi. Wannan kuskure ne. Da kyau mutum ya nemi wata sana’a ko kasuwanci mai ƙarfi sannan ya yi amfani da social media a matsayin hanyar tallata shi.
Amma idan ka ajiye duk wani aiki saboda kawai kana sa ran YouTube ko Facebook ko Website za su rika biyan ka – ka yi kuskure. Saboda lokaci guda za su iya rufe maka shafi ko asusun ka, kuma ba wani abu zaka iya yi.
Ga masu ƙoƙarin gina channel ko website don samun kuɗi, kada ku sadaukar da 100% lokaci da hankali kai tsaye. Sai shafin ya ginu sosai sannan kuma sai wani lokaci baya su duba ko sun amince da shi kafin su fara biyan kuɗi.
Musamman YouTube da website su na da wahalar samun amincewa. Zaka iya shafe shekaru kana ƙoƙari amma su ƙi amincewa. Wani lokaci, tun a lokacin da kake gina shafi matsaloli sukan taso, daga baya kuma su ce baka cika sharudda ba duk da ka gama gina komai.
Misali, zaka iya ganin Google na saka talla a channel ɗinka, amma kai baka ma yi apply na AdSense ba. Sai wasu su ɗauka cewa kana samun kuɗi, alhali kai baka ko sanin yadda ake apply ba. Wannan yana jefa wasu cikin ruɗani.
Shawarata ita ce: kada a bari online ta hana mutum yin kasuwanci na gaskiya. Idan ka bar kasuwanci saboda kana sa ran za su biya ka – to ka ruɗi kanka. Koda sun fara biya ma, babu tabbaci. Zai yiwu su rufe asusun ka ko shafi ba tare da wata dama ba.
Ka fi dacewa ka yi amfani da social media domin isar da saƙon da kake da shi ko tallata kaya. Idan daga baya suka fara biyan ka – to Alhamdulillah. Amma idan ba su biya ba, ba kai ka dogara da su ba tun farko.
– Abu Akaram ✍️
0 Comments