Wata Matashiya da Jaririyar ta yar Wata 5 Sun Shafe Watanni a Kurkukun Suleja Bayan Muzaharar Falasɗinu

Baiwar Allah da Jaririyar, ta yar Wata 5 Sun Shafe Watanni a Kurkuku Bayan Muzaharar Falasɗinu

Jamila Ibrahim, wata Matashiya ce 'yar Najeriya, na ci gaba da zaman kurkuku tare da jaririyar,ta Yar wata biyar a duniya, Fateema Naseema bayan kama da aka yi mata a lokacin wata muzaharar lumana da ta gudana domin nuna adawa da zaluncin da Amurka da I$r='ila ke yi wa al’ummar Falasɗinu.

Muzaharar, wadda aka gudanar ne cikin natsuwa a babban birnin Najeriya, ta fuskanci cikas daga jami’an tsaro, inda suka tarwatsa mahalarta tare da cafke mutum fiye da 200. Daga cikin su har da Jamila, wadda aka yi gaba da ita zuwa gidan wani Gidan yari dake Suleja tare da jaririyar da ke hannunta.

Kamar yadda Wakilin mu dake Jihar Neja Shafi'u Umar Jajirtaccen Matashin nan dake Kafafen Sada Zumunta Facebook Tiktok da sauran su  ya baiyana mana cewa Rahotanni daga shaidu sun bayyana cewa halin da Jamila da Yar,ta ke ciki yana cike da ƙunci da rashin kulawa, Abin takaici, har yanzu ba a gurfanar da ita a kotu ba, kuma ba a bayyana wani cikakken zargi da ake mata ba.

Wannan na faruwa ne a ƙasar da ake ikirarin kasancewa da 'yancin fadin albarkacin baki da kuma bin tsarin dimokuraɗiyya. Tambayar ita ce: Yaushe muzaharar lumana da tsinewa zalunci ta zama laifi a ƙasar da ake kiran musulunci?

Hakan ya janyo kiraye-kiraye ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta sakin Jamila Ibrahim da sauran waɗanda ake tsare dasu ba bisa Ka'ida ba.


Post a Comment

0 Comments