INSIGHT SERIES PHASE THREE (18): Q&A ON DONALD TRUMP AND HIS ADMINISTRATION
In January 2025, a thoughtful friend asked me deep questions about what might happen if Donald Trump returned to power. At the time, it was risky to speak openly, but now — following Trump’s peace efforts with Yemen and tensions with Netanyahu — I can share my responses for the benefit of all.
Question: Can we say MAGA = Globalism?
Answer, No. MAGA is American imperialism, not globalism. They only care about controlling wealth. They're not concerned with religion, culture, or people’s values. They're selfish, racist, supremacist — not globalists. MAGA aligns more with neoconservatism, not neoliberalism. Trump’s ideology does not fit into globalist structures.
KEY QUESTIONS & ANSWERS
1.What if Trump aligns with Russia in dealing with Iran? Russia will back Iran — even militarily, if needed. But initially, Trump will rely on pressure tactics and sanctions, not direct war.
2. How will Trump deal with Europe?, He will confront them economically and militarily. NATO will be weakened. If they resist, he might even pull the U.S. out of NATO.
3. What about Israel? Israel is weakening ideologically. Its foundation (like the Holocaust narrative) is being questioned. But physical collapse isn’t imminent yet.
4. China–Iran relations? Their bond will strengthen, especially under joint pressure from Trump. They might enter into new security alliances — including with Russia.
5. Will Iran fight alone?, Not this time. If war breaks out, Iran could receive military support from Russia and China — depending on how intense the conflict becomes.
MORE QUESTIONS ANSWERED
Why is Trump pushing for a ceasefire, despite being pro-Israel and pro-war?
He isn’t pro-war globally. He’s a realist and businessman. If a war doesn't benefit America financially, he won’t support it.
What happens when the Lebanon ceasefire ends?
He might attempt to renew it. But there’s no guarantee. If not, conflict could escalate.
Will Trump change America? Yes. If he survives and sticks to his strategy, America will undergo significant transformation. The world might experience a brief sigh of relief.
ƘARIN HASKE MARHALA TA UKU (18): TAMBAYA DA AMSA AKAN DONALD TRUMP DA HUKUMARSA
TAMBAYA DA AMSA | SHAMSUDEEN HASSAN ZURU | 9/5/2025
HAUSA VERSION
A watan Janairu 2025, wani aboki mai zurfin tunani ya tambaye ni game da komawar Trump mulki. Ya na cikin ruɗani game da tasirin hakan kan duniya, musamman game da geopolitics da geostrategy. A yau zan bayyana tambayoyinsa da amsoshin da na bashi, cikin sauƙi da fahimta.
Tambaya: Zamu iya cewa MAGA = Globalism?
Amsa: A'a. MAGA ba globalism ba ce. MAGA American imperialism ce — burinsu shi ne su kwace arziƙin wasu.
Ba sa damu da al'adu, addini ko zamantakewa. Manya ne masu girman kai, son kai da wariyar launi. MAGA da neoliberalism ba sa tafiya tare. MAGA ta fi kusa da neoconservatism — ra'ayin da ke son sarrafa duniya amma ba tare da shigar da kowa cikin tsarin rayuwarsu ba.
TAMBAYOYI DA AMSOSHI (ƘARIN BAYANI)
1. Menene zai faru idan Trump ya jawo Rasha a jikin Iran? Amsar da na bayar: Rasha za ta goyi bayan Iran sosai. Idan har Amurka ta kai hari, Rasha na iya shiga gaba ɗaya. Amma da farko Trump zai fara da takunkumi da barazana, ba da harin kai tsaye ba.
2. Yaya dangantakar Trump da Yammacin Turai?
Zai matse su ta tattalin arziki da tsaro. NATO zai rauni sosai. Idan suka takura masa, yana iya ficewa gaba ɗaya daga kungiyar.
3. Isra’ila fa? Isra’ila na cikin rauni, musamman daga ɓangaren ra’ayi da akida. Amma faduwarta a matsayin ƙasa ba ta gabatowa ba tukuna. Yanzu dai tsarin su ne ke rushewa a hankali.
4. China da Iran fa? Dangantaka za ta ƙara ƙarfi saboda matsin da Trump zai yi musu. Zai haɗe su gaba ɗaya, har su kulla sabbin yarjejeniyoyi da Rasha.
5. Iran za ta yi yaƙi ita kaɗai? A'a. Idan yaƙi ya ɓarke, za ta samu tallafi daga Rasha da China — musamman idan har Trump ya cika barazanar da yake yi.
WASU TAMBAYOYI DA AMSOSHI
Me yasa Trump ke neman ceasefire alhali shi da Netanyahu dukkansu suna goyon bayan yaƙi?
Trump ba mai son yaƙi bane idan Amurka ba za ta ci riba ba. Shi realist ne kuma ɗan kasuwa — yana kallon komai ta fuskar riba da asara.
Me zai faru idan kwana na ceasefire a Lebanon suka ƙare? Zai iya kokarin sabunta yarjejeniya, amma babu tabbaci. Idan ba haka ba, rikici zai iya ƙara tsananta.
Idan Trump ya dawo, zai canja Amurka?
Eh. Idan bai fāɗa tarkon su ba, ko kuma ba su kashe shi ba, to Amurka za ta sauya matuƙa. Duniya ma za ta huta na ɗan lokaci.
0 Comments