“After Capturing Boko Haram's Real Leader, I Was Retired, Arrested, and Detained” – Major General Danjuma Ali-Keffi Speaks

Creadt: Picture Google Search 🔍

“After Capturing Boko Haram's Real Leader, I Was Retired, Arrested, and Detained” – Major General Danjuma Ali-Keffi Speaks

In a powerful letter to President Bola Ahmed Tinubu, retired Major General Danjuma Ali-Keffi has opened up about a shocking experience following a key success in Nigeria's war on terror.

According to the General, after he led a top-level operation that captured major Boko Haram figures—including what he called the actual leader of the group—he was not honored. Instead, he was forced into early retirement, arrested, and held in solitary confinement for 64 days.

Ali-Keffi once served as Commander of the Nigerian Army's 1 Division and was appointed to lead “Operation Service Wide,” a presidential anti-terror mission. This operation reportedly exposed not only Boko Haram's leaders but also revealed their sponsors—some of whom are top government officials, military leaders, and major financial players.

“The moment we began to expose these financial networks, we faced serious backlash,” he wrote. He claims that some powerful figures tried to shut down the investigation and silence those involved.

Even more alarming, Ali-Keffi hinted at foul play in the 2021 plane crash that killed Nigeria’s former Chief of Army Staff, Lt. Gen. Ibrahim Attahiru. He stated that Attahiru supported the mission and was committed to fighting terror financiers. He called on President Tinubu to reopen the investigation into the crash and the suppression of anti-terror efforts.

This whistleblower account has sparked nationwide debate and raised tough questions:
Who truly profits from insurgency? Why are patriots being punished?

Until Nigeria confronts these issues openly, the war on terror may continue to suffer—not from lack of courage, but from betrayal within.

HAUSA VERSION

“Bayan Kama Shugaban Gaskiya na Boko Haram, Aka Kore Ni, Aka Kama Ni, Aka Tsare Ni” – Janar Danjuma Ali-Keffi Ya Bayyana

A cikin wata takarda mai zafi da ya aika wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tsohon babban hafsan soji, Janar Danjuma Ali-Keffi, ya bayyana abin da ya faru da shi bayan nasarar kama manyan 'yan Boko Haram.

Janar ɗin ya ce bayan ya jagoranci wata kwararrar runduna da ta kama shugabannin Boko Haram—ciki har da wanda ya kira “gaskiyar shugaban kungiyar”—ba a ba shi yabo ba. A maimakon haka, an tilasta masa ya yi ritaya, an kama shi, kuma an tsare shi shi kaɗai har na tsawon kwanaki 64.

Ali-Keffi ya shugabanci Rundunar Sojin Najeriya ta 1 (1 Division), sannan aka ɗora masa jagorancin “Operation Service Wide”, wani bincike da Fadar Shugaban Ƙasa ta amince da shi don yakar ta’addanci. Wannan aiki ya bankado ba kawai shugabannin Boko Haram ba, har da masu ɗaukar nauyinsu daga cikin gwamnati, sojoji, da manyan bankuna.

“Da zaran muka fara fallasa hanyar kuɗin ta’addanci, suka fara ramawa,” in ji shi. Ya ce wasu manyan mutane daga cikin gwamnati da wajen gwamnati suka yi gaggawar dakatar da binciken da kuma rufe baki ga wadanda ke cikinsa.

Abin mamaki ma, Janar ɗin ya nuna damuwa kan hatsarin jirgin da ya kashe tsohon shugaban hafsoshin soja, Lt. Gen. Ibrahim Attahiru, a 2021. Ya ce Attahiru ya goyi bayan aikin nasu kuma yana da niyyar yaki da masu daukar nauyin Boko Haram. Ya bukaci Shugaba Tinubu da ya sake bude bincike kan hatsarin da kuma yadda aka sabotaje kokarin yaki da ta’addanci.

Wannan bayani daga bakin wanda ya san abin da ke faruwa ya tayar da ƙura a fagen tsaro. Yana tambayar wasu muhimman abubuwa:
Waye ke amfana da wannan rikici? Kuma me yasa ake hukunta masu gaskiya?

Sai an yi gaskiya da tsabta, yaki da ta’addanci ba zai ci gaba da nasara ba—ba saboda rashin ƙwazo ba, amma saboda cin amanar da ke cikin gida.

Post a Comment

0 Comments