Labaran Yau Talata 29/08/2023CE - 12/02/1445AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar.
Gwamnatin tarayya ta umurci a ba dakataccen shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, damar ganin lauyoyi da yan uwansa.
Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta lalata wasu haramtattun wuraren tace danyen mai da jiragen ruwa a jihar Rivers.
Rundunar Soji dake Enugu ta gargaɗi sojojin da aka tura juhar su guji karɓar kuɗaɗe daga hannun direbobi, kuma su daina aikata duk wani abin da zai zubar da darajar aikin soja.
Ministar Al'adu da Fahasa ta Nijeriya ta ce watanta 8 da soma bautar kasa kuma babu wata doka da ta hana shugaban kasa nada mutumin da ke yin hidimar kasa kan mukami na siyasa.
Farfesa Bem Angwe, dan takarar gwamnan NNPP a Benue a zaben 2023 ya fice daga jam’iyyar.
Kamfanin rarraba Wutar Lantarki da ke Jos ya ce kwastomominsa a jihohin Filato, Bauchi da Gombe za su fuskanci matsalar wutar lantarki daga ranar 28 ga watan Agusta zuwa 2 ga watan Satumba.
An dakatar da Ministar Harkokin Wajen Libya bayan ta gana da takwaranta na Isra'ila.
Sojojin Nijar sun katse lantarki da ruwa a ofishin jakadancin Faransa.
Za a haramta wa mata sanya abaya a makarantun Faransa domin hakan ya saba wa dokokin kasar.
Ɗan adawar Zimbabwe ya yi iƙirarin cin zaɓe duk da nasarar Mnangagwa.
Taliban ta hana mata shiga wurin shaƙatawa na Band-e-Amir a Afghanistan.
Harin masu iƙirarin jihadi ya kashe yarinya a Mali.
West Ham ta kammala sayen dan wasan Ajax Mohammed Kudus a kan $48m.
Manchester City, ta kusa kammla cinikin Matheus Nunes daga Wolves bayan mika tayin da ya dace da dan wasan.
Akwai yiwuwar Joao Felix, ya maye gurbin Mohamed Salah, wanda zai koma Saudi Arabiya da take leda.
A karon farko an bai wa Virjil van Dijk jan kati a Liverpool a gasar Premier League ranar Lahadi a gidan Newcastle United, St James Park.
Joint Our Watsapp group Domin samun Labaran gida Nigeria dakuma waje👇👇
https://chat.whatsapp.com/HDQNliBg28NCWccsxhiVo0
.jpg)
.jpg)

0 Comments