Labaran Yau Lahadi 06/08/2023CE - 17/01/1445AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar.
Majalisa ta ɗaga zaman tantance ministoci zuwa Litinin.
'Yan majalisar Dattawa sun tilasta wa wanda za'a tantance a matsayin minista daga jihar Ogun Dr. Bosun Tijani neman afuwarsu da kuma 'yan kasa game da wasu kalamai da ya yi a shafukan sada zumunta a baya.
Yajin aiki: Likitocin Najeriya sun shirya gudanar da zanga-zanga a kowacce rana.
An hallaka Mista Adeniyi Sanni, mai taimakawa Sanata Solomon Adeola a jihar Legas.
Ganduje, ya ce surutan da mutanen Jihar Kano suka rika yi a kafafen sada zumunta kan nadin Maryam Shetty ne suka sa Shugaban Kasa ya canza shawararsa a kan nada ta minista.
Gwamnan Kano Abba K. Yusuf yace su na cigaba da bincike kan Abubakar Idris (Dadiyata) da ya bace a 2019.
Wani kasurgumin mai laifi da ake nema ruwa a jallo, Nasiru Abdullahi wanda aka fi sani da Chile Maidoki, ya mika wa hukuma kansa a Jihar Kano.
Bacewar gawar wata dattijuwa mai shekara 63 a yayin da ake shirin gudanar da jana’izarta a ranar Asabar ya haifar da rudani a Jihar Ondo.
Saudiyya ta umarci 'yan kasarta su fice daga Lebanon.
MDD ta yi gargadi game da tabarbarewar ayyukan jin kai a Jamhuriyar Congo.
Shirin ECOWAS na tura sojoji Nijar yana tangal-tangal.
Tsohon Firaministan Pakistan Imran Khan ya nemi magoya bayansa su yi zanga-zanga bayan kama. shi
Aljeriya da Majalisar dattawan Najeriya su ne na baya-bayan nan da suka ki amincewa a yi amfani da karfin soji kan dakarun da suka yi juyin mulki a Nijar yayin da wa'adin da ECOWAS ta ba su don mika mulki ke cika.
Brighton ta amince da yarjejeniyar da Mohammed Kudus, daga Ajax a kan kudi fam miliyan 34.5.
Arsenal za ta fafata da Man City a kofin Community Shield a yau Lahadi.

0 Comments