DA DUMI DUMINSA: Tinubu Baiyi karatun Firamare da Sakanfare ba, Atiku Abubakar ya faɗawa Kotu

DA DUMI DUMINSA: Tinubu Baiyi karatun Firamare da Sakandare ba, Atiku Abubakar ya faɗawa Kotu






Ya Akayi Ka Samu Shiga Jami'a ba tare Da ka Kammala Karatun Firamare da Sakandare ba?" Atiku Yayi Tambaya kan Tarihin ilimin Shugaba Bola Tinubu.


Ɗan Takarar Shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya kalubalanci Shugaba Bola Tinubu kan tarihin karatunsa a jami’ar Jihar Chicago (CSU) dake ƙasar Amurka.


Kwanan nan, Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya shigar da buƙata Gaban wata kotun Amurka ta tilasta wa CSU sakin Bayanan Karatun Tinubu.


Takardun Shaidar Tinubu sun nuna cewa ya sami digiri na farko a fannin kasuwanci, lissafin kudi, da Gudanarwa Daga CSU a Shekarar 1979.


Da yake bayyana ra’ayinsa a Shafinsa na Twitter, Atiku yayi la’akari da yadda Tinubu zai iya zuwa Jami’ar Jihar Chicago ba tare da kammala Karatun firamare da sakandare ba.


Atiku ya cigaba da cewa, “Na farka da safiyar yau ina mamakin yadda muka samu cikin wannan yanayi mai cike da daure kai, a Shekarar 1999, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yayi ikirarin cewa ya halarci makarantar firamare ta St. John dake Aroloya, Legas, Sai makarantar yara ta Gida dake Ibadan. Ya ambato. Kwalejin Gwamnati Ibadan, Kwalejin Richard Daley, da Jami'ar Jihar Chicago a Matsayin cibiyoyin da Ya Halarta A tafiyarsa ta ilimi."


“Abin mamaki, a Shekarar 2023, Tinubu ya bayyana cewa ya halarci Jami’ar Jihar Chicago ne kawai, Na tsinci kaina cikin dimuwa, ta yaya hakan zai yiwu? Nayi imanin cewa duk ‘yan Nijeriya masu kyakkyawar niyya ya kamata su shiga cikin rudani Game da furucin da Tinubu ya yi cewa bashi da ilimin firamare da sakandare. , duk da cewa yayi digirin digirgir, za ka iya tambayar Tinubu ta yaya ya cim ma hakan, Domin ya samo Daga hazakarsa."

Post a Comment

0 Comments