Labaran Yau Talata 06/06/2023CE - 08/11/1444AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar.
https://www.msztopnews.com.ng/2023/06/labaran-yau-talata-06062023ce.html
Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa ya ce za a kafa kwamitin hadaka kan batun karin albashin ma'aikata.
NLC da TUC sun fasa shiga yajin aiki kan cire tallafin fetur a Najeriya. saidai Kotu ta dakatar da ƙungiyoyin daga shiga yajin aiki.
Ma'aikatan lafiya a Najeriya sun janye yajin aiki.
Shugabannin kananan hukumomi 17 sun kalubalan ci matakin Gwamnan Filato na dakatar da su.
Majalisar dattawa ta zargi ofishin Akanta Janar na kasa da kin biyan bashin da aka ba ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnatin tarayya.
Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero ya kai wa shugaban Najeriya, Bola Tinubu ziyara a fadar gwamnati da ke Abuja.
Ƴan sanda sun kama masu satar kaya' a inda ake rusau a Kano.
Wani mutum da ake tuhuma da laifin sata ya tsallake tagar kotu kuma ya gudu bayan an ba da umarnin tsare shi a gidan yari a jihar Ondo.
Hukumar EFCC ta gurfanar da wasu ma'aikatan Banki guda 2 da Karin wasu 2 gaban Kotu anan Kano, an gurfanar dasu gaban Shari'a bisa zargin sacewa wani Customer Banki Naira Miliyan 20.
Ƙungiyar Ƙasashe Masu Arzikin man Fetur ta OPEC tare da ƙawayenta sun amince da rage ganga miliyan 1.393 na man da suke fitarwa zuwa kasuwannin duniya a kowacce rana.
China za ta sanya na'urori a ɗakunan jarrabawa domin hana yin satar amsa.
Ƴan sanda sun cafke wasu mutum hudu dauke da kasusuwan jikin dan Adam a Jihar Gombe.
PSG, ta doke Chelsea wajen daukar dan wasan tsakiya na Uruguay Manuel Ugarte, mai shekara 22 daga Sporting Lisbon.
Liverpool, na son biyan Barcelona yuro miliyan 35 domin daukar dan wasan tsakiya na Ivory Coast Franck Kessie, mai shekara 26.

0 Comments