Labaran Yau Litinin 05/06/2023CE - 16/11/1444AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar.
https://www.msztopnews.com.ng/2023/06/labaran-yau-litinin-05062023ce.html
Shugaba Bola Tinubu zai zauna da zaɓaɓɓun Sanatoci da ƴan majalisar wakilan tarayya da ke karkashin jam’iyyun hamayya.
Ƴan bindiga sun kai hari wasu ƙauyukan jihar Zamfara, inda suka kashe mutane da dama tare da sace ƴan mata fiye da 30 a ƙaramar hukumar Maradun.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya jagoranci rushe tsohon otal din Daula a daren jiya, sannan suka tunkari sansanin Alhazai dake Hajj camp.
Biyo bayan jita-jitan mutuwar gwamnan Jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, Gwamnatin jihar ta bukaci jama’ar jihar da su yi watsi da wanan jita-jitar tare da cewa Gwamnan yana raye.
Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Borno, Alhaji Usman Jidda Shuwa, ya riga mu gidan gaskiya.
Tsohon gwamnan jihar Nasarawa,Sanata Tanko Al Makura, yace ya janye karar da ya shigar bagan kotun zaɓe dake Lafia ne saboda samar da zaman lafiya a jihar.
Erdogan ya nada tsohon mataimakin firaiminista Cevdet Yilmaz a matsayin sabon Mataimakin Shugaba Kasa.
Kasar Sweden ta ayyana jima’i a matsayin daya daga wasannin da ta halasta, kuma ta shirya tsaf don gudanar da gasar a mako mai zuwa.
Firaministan Indiya Narendra Modi ya ci alwashin ɗaukar tsattsauran mataki kan waɗanda aka samu da sakaci a htsarin jirgin daya afku a ƙasar.
Dakarun RSF sun ƙwace cibiyar adana kayan tarihi ta Sudan.
Ancelotti ya fadawa shugabannin Real Madrid cewa ya na son dauko dan wasan Tottenham da kuma Ingila Harry Kane.
Kungiyar Al-Hilal ta Saudi ta na sa ran sanarda daukar dan wasan gaba na Paris St-Germain da kuma Argentina Lionel Messi, mai shekara 35

0 Comments