Labaran Yau Alhamis 08/06/2023CE - 19/11/1444AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar.
https://www.msztopnews.com.ng/2023/06/labaran-yau-laraba-07062023ce.html
Shugaba Tinubu ya rantsar da sabon sakataren gwamnatinsa.
Majalisa ta bukaci Tinubu ya hukunta masu a hannu a damfarar Nigerian Air.
Gwamnonin jihohi sun goyi bayan cire tallafin man fetur a Najeriya.
Majalisar Dattawa ta amince da kudirin kafa hukumar fansho ta ƴan Sanda.
Majalisar Wakilai ta yi zamanta na karshe a yau Laraba, gabanin sabuwar majalisar da za a rantsar ranar Talata mai zuwa.
An fara sauraron ƙarar da APC ta shigar kan nasarar Abba Gida-gida.
Allah Ya yi wa tsohon Wazirin Kano kuma Limamin Waje, Nasir Muhammad Nasir rasuwa.
Tallafin Man Fetur: Gwamnan Juhar Edo ya kara mafi karancin albashi zuwa N40,000 tare da rage kwanaki aiki zuwa kwana uku a mako.
Gwamna Alia na jihar Benuwai ya sallami ma'aikatan da Ortom ya dauka gab da sauka mulki.
Wata Kotun Shari’ar Musulinci da ke unguwar Danbare a Kano ta aike da wani mai kidan DJ zuwa gidan kaso, saboda sakin kida da yake yi yana damun daliban wata Islamiyya.
Bata-gari sun kai hari a gidan Rediyon Jihar Kogi, inda suka kone shi, suka kuma yi awon gaba da kayayyakinsa.
Senegal ta rufe ofisoshin jakadancinta da ke kasashen waje.
Dan bindiga ya bude wuta kan masu halartar taron yaye dalibai a Amurka.
Fadar Vatican ta sanar da cewa za a yi wa fafaroma Francis tiyata sakamakon wata jinya da yake fama da ita a cikinsa.
Ghana ta yi wa 'yan gudun hijirar Burkina Faso 3000 rajista.
Rwanda ta kori fiye da sojoji 200 daga aiki.
Lionel Messi zai koma taka leda a gasar kwallon kafar Amurka a Inter Miami, bayan da ya bar PSG a kakar nan.
Dan wasan tawagar Argentina, Angel Di Maria ya bar Juventus, bayan kaka daya da ya buga wa kungiyar tamaula.
Real Madrid ta kulla yarjejeniya da ɗan wasan Borussia Dortmund Jude Bellingham kan kudi Yuro miliyan 103.
Dan wasan Arsenal Bukayo Saka ya ziyarci kakanninsa a Jihar Kwara.

0 Comments