Labaran Yau asabar 03/06/2023CE - 14/11/1444AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar.
https://www.msztopnews.com.ng/2023/06/labaran-yau-asabar-03062023ce.html
Za a biya ’yan majalisa masu barin gado biliyan 30 a matsayin ‘kudin sallama.
EFCC ta tsare tsohon gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, da tambayoyi kan zargin wawure N4bn.
Ƙungiyar Ƙwadago ta ce a tilas a soke ƙarin kuɗin mai, an shammaci ƴan Najeriya.
Yan sanda a Legas sun cafke wata mata tuhumarta da yunƙurin siyar da jaririnta kan kudi dubu 300 Amma tace matsalolin rayuwane suka sa
Sokoto: Ƴan banga 8 sun rasa rayukansu a wata arangama da ƴan bindiga.
Dakarun sojoji sun samu nasarar ceto mutum 10 waɗanda aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara.
Ƴan sanda sun dakile yunkurin muggan ƴan bindiga a yankin Bindawa a jihar Katsina.
Kafar Daily Trust ta yi watsi da da'awar bankin CBN da ke karyata rahoton kafar kan yadda bankin ya karya darajar Naira zuwa 631.
Gwamnan Katsina Dr. Dikko Radda Ya Rufe Duk Asusun Ajiyar Bankin Hukumomi Da na Kananan Hukumomin Jihar.
Maniyyata daga Jihar Filato sun bayyana cewa sun shiga damuwa, saboda tun bayan saukar su Saudi Arabiya, babu jami’an kiwon lafiya ko jami’an kula da mahajjata ko ɗaya tare da su.
Amurka ta kakabawa bangarori 2 da ke rikici da juna a Sudan takunkumi.
SENEGAL: magoya bayan Sanko sun yi arangama da ƴan Sanda bayan yanke mashi hukumcin dauri.
Shugaban Amurka, Joe Biden ya yi tuntube ya fadi ana tsaka da bikin yaye dalibai a Makarantar Sojojin Amurka da ke birnin Colorado.
Bayanai daga Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da cewa matashin mawakin nan da ake kira da Mista 442, na nan da ransa a kurkuku bai mutu ba.
Ajax ba za ta tsawaita yarjejeniyar ci gaba da aiki da kocinta ba bayan da kungiyar ta kasa taka rawar da ta dace a bana.

0 Comments