Labaran Yau Alhamis 01/006/2023CE - 12/11/1444AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar.

 Labaran Yau Alhamis 01/006/2023CE - 12/11/1444AH Ga Takaitattun Labaran Duniyar.






https://www.msztopnews.com.ng/2023/06/labaran-yau-alhamis-010062023ce.html

Shugaba Tinubu ya gana da Shugaban EFCC a Fadar Shugaban Ƙasa.


NNPC ta kara farashin litar man fetur zuwa naira 540.


Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce ta kama mutum 93 kan zargin su da aikata miyagun laifuka a cikin kwanaki 3, daga jajiberi da ranar da kuma washe garin rantsar da sabon gwamnan jihar.


Kotun shari'ar musulunci a jihar Bauchi ta bayar da umarni ga jami'an tsaro sun kamo Sheikh Abdul'aziz Idris.


ICPC ta gargaɗi sababbin ƴan majalisun dokokin ƙasar da su kiyayi almundahana ko karkatar da kuɗaɗen ayyukan mazaɓu.


Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya kai ziyara Asibitin Murtala, da Madatsar Ruwa ta Challawa don ganin halin da suke ciki.


Tsohon mai ba tsohon Shugaba Buhari shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya samu sabon mukami da kamfanin jaridar The Sun.


Jami'an yan sanda sun sake mamaye zauren majalisar dokokin jihar Filato.


Gwamnan Kaduna Uba Sani ya yi sabbin nade nade 27, ya nada Sani Liman shugaban ma’aikatan fadar gwamnati.


Ƴan ta’addan kungiyar ISWAP sun sace wasu direbobin manyan motoci hudu a Jihar Borno.


An samu ambaliyar ruwa a wata hanya da ke unguwar Kabara, wacce ba ta da nisa daga Fadar Sarkin Kano.


Harin sojan saman Rasha ya lalata wani jirgin ruwan Ukraine.


Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ayyana dokar ta baci kan matsalar karancin ruwan sha a jihar ya bayar da wa’adin mako guda ga Hukumar Ruwa ta jihar da su mika bukatunsu tare da kawo karshen matsalar karancin ruwa da ake fama da ita a jihar.


Lalacewar al’amuran tsaro na ci gaba da kara yawan makarantun dake rufe kofofinsu a jihar Tilabery mai iyaka da kasashen Mali da Burkina Faso lamarin da ke shafar karatun yara sama da 70,000.


Ƙasar Togo na jagorantar taro kan amfani da takin zamani da inganta kasar noma.


Kotun kolin Ghana ta haramta noma da shan tabar wiwi a kasar.


Sonko ya bukaci daukacin magoya bayansa da su gudanar da zanga-zanga, a daidai lokacin ake dakon sanin sakamakon shari’ar da aka yi masa kan zargin aikata fyade, a ƙasar ta Senegal.


Rauni zai hana Anthony Martial buga wasan karshe na cin kofin FA.


Guardiola ya lashe kyautar gwarzon Manajan shekara na Ingila.

Post a Comment

0 Comments